Yan bindiga sun yi garkuwa da mai ɗakin dagaci da ɗansa a Kano..

Yan bindiga sun yi garkuwa da iyalan dagacin Nassarawa dake yankin ƙaramar hukumar Tsanyawa a jihar Kano.

Waɗanda ‘yan bindigar suka sace suke: Halima Kabiru mai shekaru 38 uwargidan dagacin na Nasarawa da Ɗahiru Kabiru mai shekaru 20 wanda ɗane ga dagacin.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Mamman Dauda ya tabbatar da faruwar lamarin ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN).

Leave a Comment