May 18, 2024

Mawakin nan Dauda Kahutu Rarara yayi martani ga masu sukarsa da cewa shi ba ɗan Kano bane.

A hirarsa da Freedom Radio ya bayyana dalilan da yasa aka fi ganin ya fi ɗaukar ɗumi a siyasar Kano.

Rarara ya kuma sake jaddada hasashensa na cewar Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne zai lashe zaɓen Gwamnan Kano.

Ya ce, yanzu a siyasar Kano tuni Ganduje ya dame Kwankwaso ya shanye balantana Abba.

Ya kuma yi martani kan mawaƙan da suke ganin ba za su iya haɗa hanya da shi ba a siyasa.

Mawaƙin ya kuma yi zazzaga kan abin da ya raba shi da Sha’aban Sharaɗa, inda ya ce, ya fice daga Jami’yyar ADP tare da Shugabanninta don haka yanzu babu sauranta a Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *