June 20, 2024

Tsohuwar jaruma a Masana’antar fina-finai takannywwod, Rashida Adamu Abdullahi, wadda akafi Sani da Rashida Mai Sa’a, ta yi yekuwar neman mijin aure tare da wasu kawayen ta wato

su Jamila Nagudu, inda tace duk wanda ya shirya auren na su to ya fito sun shirya.
Jarumar dai ta “kara jaddada maganar tane bayan wadda ta yi a shafukan ta, a lokacin tattaunawar su da wakilin Jaridar Dimukaradiyya.

Rashida Mai Sa’a tace “Jama’a su Sani ni Rashida Adamu Abdullahi Mai Sa’a da kawaye na su HadizaKabara da Teemah Yola da Jamila Nagudu, duk cikakkun Zaurawa ne idan akwai Mai son wata acikinmu to ya fito mun shirya.

Sai dai wasu mutanen suna ganin kamar Rashidansa wasa take matanar ba da gaske ba, Domin wasu suna ganin idan har da gaske ne wadannan mata suna neman mijin aure to bazasu rasa ba.

Duk da cewa ba lallai ne suma su samu irin mazan da suke so ba, sai dai kawai suyi hakuri da abinda suka samu,Amma kuma da yawa daga cikin matasa na
wannan zamanin zasu iya auren mace duk tsufanta matukar dai tanada kudi.

Kamar yanda suma
yawancin yan mata sukan iya auren mutum duk tsufan sa matukar dai akwai karafa a hannun sa, wato matukar dai yana da kudi.

To Rashida Mai Sa’a dai tayi kokarin sharewamutane wannan tantama, musamman wadannan suke kallon waccen magana tata a matsayin cewa ba gaskiya bace.

Inda Mai Sa’an tace “Babu maganar wasa in dai mutum ya shirya to ya same ni duk wadda ya ke so a cikinmu idan an daidaita abin ba zai zo da wahala ba, don haka maza kada su dauka da wasa
mu ke yi, mun shirya aure ga duk wanda ya shirya zai auren mu, in dai da gaske ya ke yi.

Mun samu wannan labari daga shafin
Hausaloaded.com Don haka mu dai addu’ar
mu a nan tace, Allah Ya tabbatar da alkhairi, Ya kuma hada kowa da rabon sa. Amin summa amin.

Ku Kalli Wannan Bidiyon:

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Bidiyon, Sannan Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *