May 23, 2024

Yanzu Malam Ya Bayyana Azabar Da Za’ayiwa Mace Mai Karin Gashin Kanta

A Wata Bidiyon Wa’azi Da Mukaci Karo Dashi Na Malam Aminu Daurawa Ya Bayyana irin Masifar Da Take Tattare Da Mata Masu Karin Gashin Kai.

Duk Da Dai Gashin Kai Yana Daya Daga Cikin Abunda Yake Karawa Mace Kyau Da Kuma Cikar Kamala A Wajen Mijinta.

Sai Dai Kamar Yadda Kyawun Fuska Yake Zama Baiwa Daga Allah Ba Kowace Mace Kedashi Ba, Haka Shima Gashin Kai Ba Kowacce Mace Take Dashi Ba.

Hakane Yasaka Wasu Matan Zamani Suke Yunkurin Zakewa Da Abunda Allah Bai Basu Ba, Musamman ‘Yam Matan Yanzu Wasu Sunayin Karin Gashi Wasu Kuma Suna Chanja Launin Fatar Jikinsu Domin Su Zama Kyawawa.

A Wani Bangaren Kuma Ana Samun Matayen Aure Da Wannan Dabi’ar Wajen Karin Gashi Ko Kuma Shafa Mayin Da Zai Chanja Kalar Fatarsu, Toh Amma Abunda Malam Yake Nufi Acikin Wa’azin Shine Mata Masu Saka Gashin Dabbobi Da Sunan Gashinsu Yayi Yawa.

Zamu So Mu Karbi Ra’ayoyinku A Sashenmu Na Tsokaci Akan Wannan Bidiyo, Kada Ku Manta Ku Danna Alamar Kararrawa Domin Samun Sababbin Shirye-shiryenmu Akoda Yaushe Mungode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *