May 18, 2024

Yanzu Yanzu Budurwar Da Ta Zagi Sheikh Aminu Ibrahim daurawa Auran Ta Ya Mutu…

Malam Dan Allah kayi min cikakken bayani akan Jigida da amfanin ta, Nagode.

Amsar tambayar wata Baiwar Allah (Da fatar Kin gani

Jigida, Ileke, Giri-giri ko Waist Beads abune da yake da daɗaɗɗen tarihi a ƙasashen Afrika, wanda ake da amannar cewa ta samo asali ne daga matan ƙasar Egypt, idan muka ɗauki Afrika ta yamma, musamman Nigeria za muga cewa matan su suna amfani da Jigida tsawon zamani daga mabambantan ƙabilun ƙasar tun kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka. Duk da akwai waɗanda suke da ra’ayin cewa Matan ƙabilar Yarbawa ne suka sanya Jigida ta zama sananniya a faɗin Nigeria. Mawaƙa daban-daban a Nigeria sunyi mata waƙa kamar irin su: Mamar Mawaƙa Maryam Fantimoti, dasu Mr. 442, Ola of Kano & Safa, inda suke cewa: “Wacce ba tasa Jigida, ai ko tana ruwa”

Saidai kamar yadda Google Arts & Culture ya bayyana shine, Larabawa da Portuguese sune suka fara shigo da Jigida a ƙasashen Afrika ta gabas domin Kasuwanci, tun daga ƙarni na 16 har zuwa na 18, kenan Jigida tazo ƙasashen Afrika ne kimanin Shekaru ɗari biyar baya (500 Years Back)

Akwai yanayi daban-daban da mata suke saka Jigida, ya danganta ne da ita Macen, amma dai wasu matan sukan ɗaura ta ne sannan su kawo zani ko Skirt su rufe ta, (Waɗanda suke sanya ta irin haka galibi ba zaka riƙa jin motsin ta ba idan suna tafiya ko wani abu) wasu matan kuma sai sun ɗaura Zanin ko Skirt sannan su kawo ta su ɗaura (Matan da suke sanya ta irin haka, to idan suna tafiya ko suna wani abun, zaka riƙa jin ƙarar ta) wasu kuma sukan sanya ta ne a saman kayan su, wato zasu fito da ita fili (Duk da dai Matan basu fiye yin haka ba sai wasu tsirarun ƙabilu) kazalika, wasu matan sukan sanya ta ne sannan su kawo Pant su saka a kanta (Wato Pant din zai rufe ta, amma mafi yawanci sai idan Jigidar mai round ɗaya ne) saboda Jigidar ta kasu kashi-kashi, akwai wacce za ku ganta Round ɗaya ne kawai, kuma Stones ɗinta ƙananu ne, so irin wannan itane ake sakawa sannan a kawo Pant a rufe ta, akwai kuma wacce za ku ganta ta kai naɗi 5 har zuwa sama idan aka naɗe ta ƙugu, to irin wannan ba’a sanya Pant a rufe ta. Sannan wata za kuga tana da Manyan Stones wata kuma ƙanana, ya danganta ne dai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *