May 23, 2024

Yanzu Yanzun nan Kotu ta Yankewa Mubarak UniquePikin Hukunci Akan Zagin Ganduje da Yayi.

BBC Hausa ta ruwaito yadda Wata kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa wanda suke wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala ashirirn-ashirin tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu ashirin kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma, sannan kuma kotun ta umarcesu su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.

Ku Kalli Cikakken vedion anan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *