Zan Rushe Bankunan Jihar Kano Idan Basu Karbi Tsohon Kudi Ba Cewar Gwamnan Kano Ganduje..

Ina kira ga mutanen kano dasu cigaba da hada hada ta tsoffin kuɗade, kuma suci gaba da kaiwa bankuna, sannan duk bankin daya ki karbar tsoffin kudi zamu rushe shi.

Idan kuma muka rushe zamuyi makaranta a wajen kuma saina soke duka wani lasisin bankin, cewar gwamnan jihar kano abdullahi umar ganduje.

Gwamnan kano abdullahi umar ganduje ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai na jihar kano yayin da yake bayyana musu cewa wannan hukunci daya yanke shine mafita ga bankunan dake cikin jihar ta kano.

Hakika talaka yana shan wahala sosai a wannan lokaci musamman magidanta masu kananun yara da kuma ‘yan kasuwa wanda dalilin wannan canjin kudi ya janyo sunyi asara sosai a kasar nan.

Yanzu haka dai gwamnan yace dukkan wani mai tsohon kudi yayi maza ya garzaya izuwa banki, domin kaiwa tsohon kudin shi dake fadin jihar kano ta nigeria cewar gwamnan kano abdullahi umar ganduje.

Leave a Comment