May 16, 2024

Abubuwa Biyar dake fitar da Soyayyan Namiji daga Zuciyan Mace Cikin Kankanin Lokaci

Soyayya gamon jini inji bahaushe

Akwai matukar dadi da annashuwa idan soyayya takance tsakanin masoya har karshen rayuwa, kauna da kulan dake zama a zukatan masoya ba game gari bace kuma ba abar dauka da wasa bace.

Soyayya na bukatan kulawa, raino lokaci da kuma abubuwa da yawa da ke iya sa ta sade na tsawon lokaci.

A wannan rubutun, zamu tattauna akan abubuwan dake sa son namiji ya fita daga zuciyan mace kwata kwata ga kadan daga ciki

1) Rashin kula yawan lokacin da ka ba wajen hira ko kuma kallon bal matan ka baka bata wannan lokacin balle ka fuskanci matsalan ta itama ta gane naka matsalan.

Yiwa mace rikon sakainan kashi:wasu mazan na soyayya da mace amma kiran muntoci kalilan na gagaran su. Wannan nuna halin ko inkula din nasa mace ta daina son namiji kwata-kwata.

Kalu balanta akai akai:mata basu kaunan namiji mai yawan kalu balantan su

kalu balanta nafara shiga tsakanin masoya ake samun babban matsala tsakanin ta da masoyan ta.

(Rashin biyan bukata:yawancin mata suna son suga namiji yana nuna musu yana son abin suke so koba gaskiya bane, idan sunada bukatan abu ya nuna musu shima yanason wannan abu sama da su ma amma kuma ga yanayin da ake ciki sai Allah ya kawo.

Nuna kauna: mata dayawa basu son namiji yana boye irin son da yake musu sunfi son a koda yaushe ya nuna kalan son da yake musu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *