May 19, 2024

Bidiyon Yadda Wata Budurwa Take Iskanci Dan Taja Hankalin Samari

HANTSI Hana ‘Ya’ya Mata Aure Lokacin Da Suka Bukata Kan Lalata Tarbiyyarsu

Lallai akwai babbar illa ga tarbiyar yara mata lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su.

Yan mata da yawa sun fada fikin gurbacewar tarbiya lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su.

Wani lokaci yara mata kan bukaci yuin aure, amma sai iyayesu su hana su, ko don saboda karatu ko wanda suka kawo su iyayen ba sa san su ko kuma saboda wadanda dalilai, wannan ba karamar raunata tarbiyar yuara mata ya ke yi ba.

Sakamakon hakan, sai ka ga sun fada shaye-shaye, karuwanci da kuma wasu hanyoyi wadanda ba su dace ba.

An samu wata yarinya da ta bukaci mahaifinta ya yi mata aure, kuma har ma ta kawo wanda ta ke so, amma mahaifin nan yaki, daga karshe yarinyar ta rubuta masa wasika cewa, “na tafi idan ka zo sai Allah ya yi mana shari’a.” Sai ta hau saman bene, inda ta fado ta mutu har lahira.

Haka kuma, wata ta samu mahaifinta ta bayyana masa cewa, ya yi mata aure ko kuma ta lalace ta bi duniya. Idan za a samu irin wannan lamari, to ya kamata iyaye su tashi daga barcin da suke yi wajen aurar da yaransu lokacin da suka bukata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *