May 19, 2024

Daga cikin matsalolin da ma’aurata ke fuskanta shine Munana zato da ma juna Kudin goro, tabbas akwai qarancin kyautata zato a tsakanin ma’aurata da dama.

Gefen maza :- duk abunda matar su tayi dan ta burge su, ko dan qara armashin soyayya da zamantakewar su, sai mijin ya dauka zata cutar dashi, abun anunsa take so kawai, zata mallake shi, zata damfare shi, ko tana neman wani abua wajen sa ne. Ko duk abunda tayi bata da hankali ko tunani mai kyau, ko..ko.

Gefen Mata :- duk abunda namiji ya yi sai sun dangantashi da cin amana, “namiji ba dan goyo bane” rashin kyautatawa ba’a iyan ma namiji da
dai sauransu.

Wannan dabřa na “wasu” ma’auratan yana da nasaba da yanayin al’ada, inda suka fito, qarancin wayewa, ilimin addini, zamani dana zamantakewa.

Wannan ya hana ma’aurata da dama jin dadin juna domin su ba haka suke ba alhali abokan zaman su haka suka dauke su.

Wannan ya hana ma’aurata da dama jin dadin juna domin su ba haka suke ba alhali abokan zaman su haka suka dauke su.

Matuqar zamu cigaba da munana zato ga juna, bazamu nemi ilimin daya dace wajen sanin juna ba, tabbas zaiyi wuya wasun mu su ji dadin
zaman aure.

Karku manta dan wasu haka suke ba shine ya tabbatar muku da naku ma haka suke ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *