May 16, 2024

Bayan ya aureta lokacin da mutane ke gudunta,Allah ya azurta su da samun karuwa

Bayan Allah ya azurtasu da samun karuwa

Hakika wadannan bayin Allah sun burgeni matuka, musamman matashin da yayi jarunta ya auri matashiyar wacce fuskarta ta canza sakamakon kunar wuta shafin arewa intelligence na wallafa.

Jama’a wannan shine soyayya na gaskiya, kyawun fuska ina daukarsa yaudara, domin kyan fuska wani abune kawai da yake gamsar da bukatar kwayar idanuwa

Samari da ‘yan mata watakila ba zasu fahimci wannan zancen nawa ba a yanzu, amma duk wanda yayi aure ya haihu da matarsa haihuwa daya biyu zuwa uku zai fi kowa fahimtar abinda nake nufi fa cewa kyawun fuska yaudara ne kawai, bukatar ido yake

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *